Jami'an tsaron kasar Congo sun kama wasu masu zanga zanga dake nuna kyamar shugaba Kabila a yankunan Kinshasa, Bukavu, Goma da kuma Lubumbashi yayinda suka yi gangami na jami'iyyar LUHCA a duk fadin kasar don tilastawa kwamishanan zaben kasar ya sanya sunan Himma cikin masu takara a shekarar 2017.
Hotunan Wasu Da Aka Kama A Congo Yayinda Suke Zanga Zangar Nuna Kyamar Shugaba Kabila

1
An kama wasu yan gwagwarmaya matasa na jam'iyyar LUCHA su 40 dake a Goma, ranar 31 watan Yuli na shekarar 2017

2
Masu zanga zanga sun nuna bakin cikinsu inda suke neman a gudanar da zaben shigaban kasa nan zuwa watan Disemba na shekarar 2017; ranar Litinin 31 ga watan Yuli na shekarar 2017

3
Yan sanda sun kama wasu masu zanga zanga a RDC, ranar Litinin 31 watan Yuli na shekarar 2017

4
Yan sanda na ci gaba da yin bincike akan tittunan garin Goma, ranar Litini 31 ga watan Yuli na shekarar 2017
Facebook Forum