Hotuna Kan Takaitattun Labaran Duniya Da Na Afirka a Yau
Hotuna Kan Takaitattun Labaran Duniya Da Na Afirka a Yau

5
Masu tsaron gabar tekun Italiya sun kai bakin haure 725 mafi yawancinsu ‘yan Afirka zuwa Sicily bayan da aka ceto su a tekun Meditareniya. Ranar Alhamis 30 Maris 2017.

6
Kungiyar ba da agajin kasa da kasa ta Red Cross ta fara sako kayan abinci daga jirgin sama a yankunan Sudan ta Kudu dake fama da matsananciyar yunwa. Ranar Alhamis 30 Maris 2017.

7
Wata mota dauke da bam ta fashe a Bagadaza a jiya Laraba, inda ta halaka mutane 17 kana ta raunata wasu 60. Ranar Alhamis 30 Maris 2017

8
Shugaban Afirka ta Kudu Joseph Zuma ya sha alwashin korar ministan kudinsa da ake mutunta wa, matakin da ake ganin zai raba kan ‘yan jam’iyar ANC mai mulki. Ranar Alhamis 30 Maris 2017.
Facebook Forum