A yau litinin aka ji Ministan harkokin wajen kasar Iran Manoucher Mottaki yana shaidawa Majalisar Dinkin Duniya cewa akwai rashin fahimta a zargin da ake yiwa Iran da laifin jigilar makamai ta hannun ‘yan kasuwa zuwa Nigeria inda jami’an tsaro suka chafke su bayan bincike.
Yace yanzu matsalar da hakan ta haifar an kauda ita. Idan an tuna Juma’ar data gabata ce hukumomin Nigeria suka yi barazanar kai karar Iran gaban kwamatin sulhun Majalisar Dinkin Duniya saboda keta haddin takunkumin da Majalisar ta aza mata.
A wani labarin kuma, Wani kamfanin ayyukan binciken mai na Amurka ya bada sanarwar samun nasarar gano rijoyoyin man fetur a gabar tekun kasar Saliyo.Shi wannan kamfanin mai mai suna Anadarko da cibiyarsa ke Texas Amurka ya bada sanarwa gano rijiyar danyen mai- lakabin “Mercury-1” a karkashin ruwan teku da tazarar kilomita hamsin daga bakin gabar ruwan tekun Saliyo.
Kamfanin yace zai kokarta yin aikin hadin gwiwa tare da wani kamfanin da kuma hannun Gwamnatin kasar Saliyo.