Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Kai Farmaki Kan Sansanonin Tsagera


Wasu sojojin Najeriya su na gadin shugaba Goodluck Jonathan lokacin da ya ziyarci gidan marigayi shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa a Katsina, 8 Mayu, 2010
Wasu sojojin Najeriya su na gadin shugaba Goodluck Jonathan lokacin da ya ziyarci gidan marigayi shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa a Katsina, 8 Mayu, 2010

Rundunar sojojin ta ce ta kai sumame kan sansanoni uku na tsagera a kudancin kasar yayin da wata kungiyar tsageran ta ke cewa an kashe mutane fiye da 100

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kai sumame kan wasu sansanoni uku na ‘yan tsagera a yankin kudancin kasar mai arzikin mai. Tsagera sun ce an kashe mutane fiye da 100 a wannan farmakin.

Jami’an soja sun ce har yanzu ba a samu adadin wadanda suka mutu ba.

Sanarwar da wata kungiyar tsagera wadda kusan ba a san da ita ba, Niger Delta Liberation Force, ta ba ‘yan jarida, ta ce an kashe mutane fiye da 100 a wannan farmaki da sojoji suka kai. Amma kuma babu wata hanyar gaskata ikirarin wannan kungiya.

Gwamnatin Najeriya tana kokarin murkushe tsageranci a yankin Niger Delta, inda yawan hare-hare da sace-sacen mutane suka rage yawan man da ake hakowa da kuma kudaden shigar da gwamnati ke samu.

Tsagera da dama sun ajiye makamansu karkashin wani shirin ahuwa da suka kulla da gwamnati a shekarar da ta shige. Amma wasu bangarorin kungiyoyin ‘yan tsageran su na ci gaba da gwagwarmaya, bisa abinda suka kira kokarin samarwa da mutanen yankin karin kaso na arzikin mai.

XS
SM
MD
LG