Masu zabe a kasar Iran sun sake zabar Hassan Rouhani a wani sabon wa’adin mulkin kasar.
Tashar telebijin ta kasar tace, bada wata matsala ba, Rouhani ya kada abokin takararsa mai matsancin ra’ayi Ebrahim Raisi, a zaben shugaban kasan da aka kamalla inda shi Rouhani din ya kwashe 57% na kuri’iun, yayinda Raisi ya karkare da 38%.
Mutane hudu suka tsaya takarar shugabancin kasar.
Saboda dimbin mutanen da suka fito jefa kuriu’ar, ala tilas aka kara tsawaita awowin gudanarda zaben a jiya Jumu’a har zuwa 12n dare, inda wasu masu jefa kuri’a suka share sa’oi suna jiran su yi zaben.
Rumfunan zabe fiye da dubu 60 aka kakafa don baiwa mutane miliyan 56 damar jefa kuri’unsu a duk kasar.
Facebook Forum