Shugaban Kasa Hassan Rouhani na iya fuskantar kalubale sosai daga masu tsatstsauran ra’ayi wadanda suka soki lamirin yadda ya rike tattalin arzikin Iran da kuma yarjejeniyar nukiliyar da ya cimma da kasashen Yamma.
Rouhani ya sami nasarar karfafa Siyasar sa ne ta shirya yarjejeniyar Nukiliya. Wacce ta jawo sassauci akan takunkumin harkokin tattalin arzikin da aka dora akan Iran. Amma wanda ke kalubalantar sa a zaben, Ebrahim Raisi, ya kalubalanci yarjejeniyar saboda ta bar takunkumai akan harkokin Bankuna da kuma harkokin kudi.
Ana ganin Rouhani a matsayin wanda masu fashin baki suka fi so da kuma kadan daga cikin kuri’un jin ra’ayi da aka gabatar. Haka kuma ya na da tarihi a bangaren san a dukkanin shuwagabannin da suka gabata an sake zaben su tun daga shekarar 1981.
Amma idan Rouhani ya kasa samun Kuri’u mafiya yawa a yau Juma’a daga sauran yan takarar hudu, za’a sake gabatar da zaben ne a karo na biyu tsakanin mutane biyu da suka fi samun yawan kuri’u.
Ra’isi mai tsatstsauran ra’ayi yana yi takara ne akan harkokin tattalin arziki, inda yayi alkawarin kirkirar sabbin miliyoyin aiyukan yi da kuma gyara yawan rashin aikinyi na kasar da yakai kaso 12,7 cikin dari. Ana kallon Ra’isi a matsayin mafi kusanci ga Ayatollah Ali Khameni, Babban Shugaban Majalisar Iran, duk da dai Khameni bai fito fili ya yiwa Ra’isi Kamfe ba.
Facebook Forum