Biyo bayan gargadin na hafsan soji, Jakadan Birtaniya a Najeriya shi ma ya gargadi 'yan Najeriya cewa tsarin dimokradiya a Najeriya wani abu ne mai tsada da za'a yi wasa dashi ba.
Inji Jakadan duk wadanda basu gamsu da salon mulkin wannan gwamnatin ba su bi tsarin dimokradiya wajen kawar da ita ko su jira lokacin zabe amma ba ta hanyar juyin mulki ba da karfin soji.
Kwararre kan sha'anin harkokin kasa da kasa Ambassador Suleman Dahiru ya kalli gargadin ta fuskar diflomasiya.
Yana mai cewa kasashen irin su Birtaniya suna da mutanensu dake yin bincike da suka san abubuwan da su keyi. Yace su ba zasu sani ba amma Birtaniya da Amurka zasu sani. Yace maganar jakadan daidai take saboda idan ma akwai wadanda suke tunanen yin canjin gwamnati yanzu an nuna masu cewa an gane manufarsu.
Ambassador Suleman Dahiru yace sojojin dake zuwa wurin 'yan siyasa a bincikesu sosai.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum