A hirar da wakiliyar Muryar Amurka tayi da wasu mazauna garin Potiskum, Gambo Barau Potiskum yakecewa, “abin ya faru da missalin karfe goma sha daya na yammacin yau, akwai yan uwanmu suna muzahara sun dawo daga cikin gari bayan zagaye zasu koma sansaninsu nan faudiya anzo saitin gidanmu kofar gidan Alhaji Chadi, sai mukaji karan bom ya tashi.”
Ya dai kara da cewa mutane dayawa sun rami raunika harma wasu sun mutu, Barau dai yace a yanzu dai basu san ko suwaye suka kai wannan harin ba. Amma wani mutum da ake tsargi kamar shine yazo da bom din ya yanka a guje sai mutane suka bishi suka fara dukansa har saida jami’an tsaro suka karaso suka daukeshi.
Saurari hirar wakilar Muryar Amurka Maryam Dauda da wasu 'yan garin Potiskum.