Wani wanda ya bayyana kansa da cewa ya na daga cikin sojojin Nijeriya da su ka gudu, lokacin da ‘yan Boko Haram su ka kai hari a garin Mubi na jihar Adamawa, ya ce rashin isassu da ingantattun makamai ne ya sa su gudu saboda babu yadda za su tinkari ‘yan Boko Haram da kananan makamai kuma marasa inganci.
Sojan ya ce cikin makaman da ‘yan Boko Haram ke da su har da “AA” da “RCC.” Ya ce kodayake an turo Karin sojoji don su taya su, hakan bai taimaka ba saboda su ma wadanda aka sake turowa din ba su da irin makaman da ‘yan Boko Haram ke da su. Ya ce kafin su gudu sai da su ka fafata da ‘yan Boko Haram na tsawon sa’a guda; kuma ya ce sun kashe ‘yan Boko Haram da dama.
Sojan ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta wadata sojojinta da isassun kuma ingantattun makamai muddun ana so a kau da ‘yan Boko Haram.
Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Ibrahim Abdul’aziz, wanda ya turo wannan rahoton, ya ruwaito wasu ganau na cewa har ma ‘yan Boko Haram sun fara wa’azi da nuna ikonsu a garin na Mubi.
Koriya Ta Arewa ta tabbatar cewa ta kama wani ba-Amurke dan yawon bude ido tun wata guda da ya gabata, ta kuma ce tuni ma ya roki gabafar laifukan da ya aikata a yayin yakin Koriya da kuma rashin biyayyar da ya nuna ma kasar a yayin ziyarar da ya kai a baya bayan nan.
Kafar Yada Labaran Koriya Ta Arewa Ta fadi yau Asabar cewa Merill Newman dan shekaru 85 da haihuwa ya yi kokarin ganawa da wasu sojojin da su ka tsira da ransu wadanda ya harar da su don su yaki Koriya Ta Arewa a yayin yakin na Koriya.