Su kuma 'yan jamiyyar PDP cewa suka yi sun shirya tsaf domin kwace mulkin jihar daga hannun jam'iyyar APC.
A wani gagarumin taro da jam'iyyar APC reshen Lafiya ta shirya inda ta gayawa gwamnan jihar Umaru Tanko Al-Makura ya sake tsayawa takara tace ba gwamnan kadai ba a duk fadin Najeriya tana ganin haken darewa kan mulkin kasar a zaben 2015. Jami'iyyar ta gayyato 'ya'yan jam'iyyar daga sassa daban daban na Najeriya.
Magoya bayan APC cewa suka yi ba ma a jihar Nasarawa kadai ba, jam'iyyar zata lashe duk zabukan da za'a gudanar shekara mai zuwa. Tsohon ministan babban birnin tarayya Malam Nasiru El-Rufai yace yana da tabbacin nasarar jam'iyyarsu a zabuka masu zuwa. Dalili ke nan ya kira gwamnan jihar Nasarawa ya sake fitowa takara domin ya cigaba da aikin alheri da ya fara a jihar.
El-Rufai yace ita PDP ba zabe take ci ba. Satar zabe take yi. Yace 'yan Najeriya sun gaji da Boko Haram da Ebola da PDP ta kawo.
Babban bako mai jawabi Injiniya Buba Galadima yace jam'iyyarsu zata bada mamaki a zabe mai zuwa. Ya kira mutane kada su ba duk wanda ya nemi mulki sai dai wannda su suka kira ya zo ya mulkesu. Yayi misali da abun da ya faru a kasar Burkina Faso. Sabili da haka tunda jama'a sun yadda da mulkin gwamna Tanko Al-Makura babu wani mutum da zai iya kwacewa jama'a gwamnansu.
Tsohon gwamnan jihar Adamu Abdullahi yace jama'a suka ga ya dace Umaru Tanko Al-Makura ya cigaba da mulkin jihar. Idan makasudin gwamnati shi ne a yiwa mutane aiki to Tanko Al-Makura ya yiwa mutane aiki kuma ya kamata a yaba mashi. Idan wani ya zo ba zai cigaba da aikin gwamnan ba.
Su ma 'yan jam'iyyar PDP ba'a barsu a baya ba kasancewar yadda 'yan takaran gwamna suka fito kamar yadda shugaban jam'iyyar reshen Nasarawa Chief Yunana Iliya ya shaidawa Muryar Amurka. Yace suna da 'yan takara takwas amma yana yin kokarin sasantasu. Yace zaben da aka yi na kananan hukumomi sun nuna PDP zata ci domin sun kada APC a kananan hukumomi goma sha daya. Kowanene suka tsayar zai kada Tanko Al-Makura.
Wasu 'yan jam'iyyar sun bayyana ra'ayoyinsu akan shirin da PDP tayi. Alhaji Danjuma Musa Karkuwan Dedere yace idan mutum yace talakawa suna tare da Al-Makura su wanene talakawan. Talakawan ne suke yiwa gwamnatin Allah ya isa domin tun kafuwarta mai mata ma bai san inda matarsa take ba. Manomi baya iya zuwa gonarsa haka ma makiyayi bai san yadda zai yi kiwo ba sabili da tashin hankalin da ya addabi jihar. Barde Agwai kuwa cewa yayi mulkin ma ya riga ya shiga hannunsu.
Ga rahoton Zainab Babaji.