Jami’an tsaro a Masar sunce mutane 305 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu ‘yan bindiga suka hari wani masallacin Juma’a dake cike da mutane a Arewacin yankin Sinai. Ashirin da biyar daga cikin wadanda suka mutun kananan yara ne.
Ofishin babban lauyan gwamnatin Masar yace ‘yan bindigar tsakanin su 25 zuwa 30 ne suka kaiwa masallacin al-Rawdah dake garin Bir al-Abed hari.
Maharan dai sun isa harabar masallacin ne cikin mota, suka tayar da bama bamai sannan suka ruga cikin masallacin, inda suka budewa masu ibada wuta alokacin da mutane ke kokarin ficewa.
Har ya zuwa yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai harin.
Wasu shaidun gani da ido sunce maharan sun harbi motar agaji, yayin da ma’aikatan agajin gaggawan ke kokarin kwashe mutanen da suka sami rauni zuwa asibiti. Kafar labaran kasar ta ce mutane 128 ne suka raunata a harin.
Facebook Forum