Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kaiwa Jamian Tsaro Hari A Pakistan


Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.
Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.

An kaiwa jerin gwanon jamian tsaro harin kunar bakin wake da yayi dalilin mutuwar mutane 5 kanawasu 20 suka ji rauni

Yau asabar wani dan kunar bakin wake ya tada bomb ga jerin gwanon motocin jamiaan tsaro a kudu maso yammacin Pakistan, wanda hakan yayi dalilin mutuwar biyar daga cikin su tare jima wasu 20 rauni.

Bomb din ya tashi ne a babban titin nan dake Quetta wuri da yake da yawan zirga-zirgan jamaa, wanda yake nan ne babban birnin gundumar Baluchistan inda suke fama da rikici.

Wannan harin dai yayi dalilin samun raunin wasu fararen kaya da dama kamar yadda mukaddashin sufeta janar na ‘yanda Abdulrazak Cheema yake cewa.

Cheema ya fada ma manema labarai cewa daga bayanan aka tattara a wurin da aka tada wannan bomb din ya nuna cewa wanda ya tada bomb din yayi likimo ne a wani hotel dake bakin hanya kafin ya aikata wannan aika-aikan.

Yace masu bincike sun sun samu wasu sassan jikin dan kunar bakin waken kuma yanzu haka suna nan suna kokarin gane ko shi wanene.

Sai dai kuma ‘yan kungiyar Taliban sun dauki alhakin aikata wannan mugun aikin, suna cewaa sun samu nasarar hallaka jamiaan tsaro da dama, Sai dai kuma sau tari kungiyar takan yi zunbuden adadin jamaar da aika-aikan su ta rutsa dasu.

Cikin ‘yan kwanakin nan ana samun karuwar tashe-tashen hankula a wannan yankin na Queta inda ake kashe mjutane mutane da dama wasu kuma aji musu rauni.

Baluschitan dai wani yankin hada-hadar kasuwanci ne da gwamnatin kasar ta Pakistan ta gina da miliyoyin kudi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG