Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Myanmar da Bangladesh sun yi yarjejeniya akan kabilar Rohingya


'Yan kabilar Rohingya dake tserewa daga Myanmar suna tsarawa ta tekun da ya raba kasarsu da Bangladesh
'Yan kabilar Rohingya dake tserewa daga Myanmar suna tsarawa ta tekun da ya raba kasarsu da Bangladesh

Kisan gillar da ake yiwa kabilar Rohingya ya kawo karshe da yarjejeniyar da kasashen Myanmar da Bangladesh suka yi wadda za ta sa 'yan Rohigyan fiye da dubu dari shida dake gudun hijira a Bangladesh samun komawa jiharsu ta Rokhine a kasar Myanmar

Myanmar da Bangladesh, sun rattaba hanu akan wata yarjejeniyar maido da daruruwan dubban ‘yan kabilar Rohingya, wadanda suka tsere zuwa Bangladesh domin gujewa azabtar da su da ake yi a jihar Rakhine da ke Myanmar, a cewar hukumomin kasashen biyu.

Myint Kyain, wanda Sakatare ne na Dindindin a ma’aikatar da ke kula da harkokin kwadago da kaurar jama’a da kuma yawan al’uma a kasar ta Myanmar, ya ce an rattaba hanu akan wata yarjejeniyar fahimtar juna a jiya Alhamis, ba tare da bada wani karin haske akan yarjejeniyar ba.

Sama da Musulmi ‘yan kabilar Rohingya dubu 600 ne suka tsallaka zuwa sansanonin ‘yan gudun hijra da ke Bangladesh.

Kasar ta Bangladesh, ta ce, nan da watannin biyu masu zuwa za a fara aikin kwaso ‘yan Rohingyan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG