Da ya ke jawabi jiya Alhamis ga Manema labarai a taron da Firaministan Turkiyya Ahmet Davutoglu ya ke jibinta a birnin Ankara, Mista Tusk yace, idan aka fara maida bakin hauren zuwa kasashen da suka fito, hakan zai karya lagon kasuwancin masu hada-hadar safarar mutanen da suke ketararwa ta ruwa zuwa Turai.
Shugaban ya yanawa Turkiyya game da hobbasarta na dada tsuke kan iyakarta da kuma sake tsaurara matakan samun Visa don ganin ta taimaka wajen shawo kan lamarin kwararar ‘yan gudun hijirar.
Shima Firaministan Ahmet Davutoglu ya fadi cewa, kar dama a yi zaton cewa Turkiyya da Girka su kadai za su iya jurewa matsalar kwararar bakin hauren da suke tururuwa zuwa Turai a kullum.
Dama Donald Tusk din ya gargadi hatsarin kwararar bakin a lokacin da ya taba ganawa da Firaministan Girka Alexis Sipras.