Wani sabon bincike ya nuna cewa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya bada bayanin yadda Koriya ta Arewa ta kaucewa takunkumin kasa da kasa kusan shekaru 10 da suka wuce. Wannan binciken ya zo ne bayan da kwamitin ke shirin jefa kuri’a akan takunkumi da za ‘a sanya wa kasar mai mulkin mallaka.
Wani rahoto da kwamiti da ke kula da saba takunkumai na Majalisar Dinkin Duniya ya rubuta, ya yarda cewa sau hudu Majalisar Dinkin Duniya na sanya takunkumi akan Koriya ta Arewa tun shekarar 2006, amma hakan bai sa gwamnatin shugaba Kim Jong daina shirin nukiliya da makamai masu linzami ba.
Bisaga gwajin nukiliya da tauraron dan’adam da Koriya ta Arewa ta kaddamar kwanan nan, da kuma dagewa da ta yi akan cewa shirin makamanta na nukiliya na da muhimmanci wajen kawas da duk wata barazana daga Amurka, rahoton ya ce akwai tambayoyi da yawa game da ko ma takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya yanzu za su yi wani tasiri.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana wurare da yawa da Koriya ta Arewa ta kaucewa takunkumi, ta kuma bayyana yadda kasar ke cigaba da cin moriya kudaden asusun kasa-da-kasa, da yi namfan ida hanyoyin jiragen sama da kuma na ruwa don sayar da kayayyakin da aka haramta.