Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ne ya bayyana hakan, a ranar Juma’a.
A cewar Kerry, za a yi gwajin shawarwarin da aka bayar gabanin wata ganawa da jami’an diplomaisiyyan Amurka da Rasha za su yi a Geneve a mako mai zuwa.
Kerry ya yi wadannan kalamai ne yayin da suka gabatar da wani taron manema labarai da takwaran aikinsa na Italiya a birnin Rome, inda Kerry ya yi kiran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da gudanar da ayyukan jin-kai a Aleppo.
Bayan kuma wata ganawa da ya yi da takawaran aikinsa na Rasha, Sergie Lavrov, Kerry ya ce ana fatan sabbin matakan da za a dauka za su kai ga samar da zaman tattaunawa tsakanin gwamnatin Shugaba bashar al- Assad na da ‘yan tawayen kasar.
Batun zaman tattaunawa tsakanin gwamnatin ta Syria da ‘Yan tawayen ya cutura, duk da yunkurin da aka faro tun daga shekarar 2014.