Hukumar binciken sararrin samaniya na Rasha yace jirgin ya tarwatse ne bayan yayi tafiyar kilomita 190 daga doron kasa.
Galibin baraguzan jirgin da kayayyaki da ya dauka sun kone a sararin samaniya. Sauran abunda ya rage bai kone ba ya fadi a wani wuri mai nisa a kasar Saberiya ba nisa daga kan iyakar kasar da Mongolia. Babu rahotannin cewa tarwatsewar ta jikkata mutane ko ta haddasa wata barna ba. Ana ci gaba da binciken musabbabin tarwatsewar jirgin.