Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Turkiya Na Kakkabe Wadanda Suka Yi Yunkurin Juyin Mulki


Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan

Dakarun kasar Turkiyya, sun tsare wasu sojoji 11 a yau Litinin, wadanda ake zargi da kai wani hari a wani otel, inda shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan ke zaune a lokacin da aka yi yunkurin juyin mulki a kasar a tsakiyar watan Yuli.

An cafke sojoji ne a kusa da wani wajen shakatwa da ke garin Marmis, wanda hakan ya biyo bayan dumbin sojojin da aka cafke da ake zargi suna da hanu a yunkurin kifar da gwamnatin Erdogan.

A lokacin dai Erdogan na zaman hutu ne a garin a ranar 15 ga watan na Yuli, inda aka yi yunkurin kifar da gwamnatinsa, kuma jim kadan bayan da ya bar otel din ne wasu sojoji suka kai samame a wurin.

Wannan lamari na kama sojojin da aka yi, shi ne yunkuri na baya-bayan nan da aka yi a ci gaba da tattara wadanda ake zargin suna da hanu a yunkurin juyin mulkin.

Shaikh Fethullah Gulen wanda gwamnatin Turkiya ta zarga da shirya juyin mulki daga inda yake zama a Amurka
Shaikh Fethullah Gulen wanda gwamnatin Turkiya ta zarga da shirya juyin mulki daga inda yake zama a Amurka

A ranar Lahadi ne dai gwamnatin kasar ta Turkiyya, ta sallami kusan sojoji 1,400, ciki har da manyan hafsoshi masu ba da shawara, kana shugaban ya maida alhakin lura da rundunar sojojin kasar a karkashin farar hula.

Fiye da mutane dubu biyar ne yanzu suka rasa ayyukansu a duk fadin kasar, kana sama da dubu 18 ke tsare wadanda ake zargi suna da hanu a yunkurin juyin mulkin da aka dora laifin akan Malamin addinin Islaman nan Fethullah Gulen wanda yanzu yake zaune a jihar Pennsylvania dake nan Amurka

XS
SM
MD
LG