An damke akalla dan jarida guda, kuma an ba da sammacin kama tsoffin manyan 'yan jarida 50 da su ka yi aiki a gidan jarida mafi girma mai suna Zaman.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce daukar mataki iririn wannan kan 'yan jarida wani abu ne mai tayar da hankali.
Gidajen jaridun gwamnati da masu zaman kansu a Turkiyya, sun ce an umurci jaridu wajen 45 da ake bugawa kullum a kasar su rufe; haka ma wasu kamfanonin dillancin labarai uku da gidajen talabijin 16. A baya ma an ba da sammacin kama 'yan jarida masu zaman kansu su wajen 42, kuma tuni 16 daga cikinsu su ka shiga hannu.