Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiya Ta Sallami Dubban Jami'an Sojojinta


Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan

Biyo bayan yunkurin juyin mulki da wasu sojoji suka yi a Turkiya wanda bai yi nasara ba, sakamakon yunkurin ya fara shafar wasu inda dubban sojoji aka sallama tare da cigaba da tsare 'yan jarida masu dimbin yawa da rufe kafofin aikinsu

Kwana daya bayan da gwamnatin kasar Turkiyya ta sallami jami’an sojan Kasarta fiye da 2,400 aka.

Majalisar kolin sojan kasar ta kuma cigaba da gudanar da wani zaman gaggawa don gano bakin zaren al'amurra bayan abubuwan da suka wakana a kasar.

'Yan jarida suka taru a harabar kotun da aka gurfanar da 'yanuwansu 'yan jarida
'Yan jarida suka taru a harabar kotun da aka gurfanar da 'yanuwansu 'yan jarida

Yanzu dai an dorawa manyan jami’an sojan kasar nauyin cike gurbin manyan hafsoshin soja masu mukaman Janar-janar guda 149, kusan rabin gungun manyan sojojin kasar mai mambobi 358, wadanda ake zargi suna da hannu a yinkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba ranar 15 ga watan nan na Yuli.

Zaman da aka yi a safiyar yau Alhamis ya hada da firayin minista Binali Yildrim da kwamandojin sojan kasa, da na ruwa da kuma na saman Turkiyya.

Haka kuma gwamnatin kasar ta rufe tashoshin talabijin guda 131, da wasu jaridu da kuma wasu kafafen yada labarai.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG