A wani rubutu da yayi a shafin jaridar New York Times, Mallam Fethullah Gulen, ya kira zargin da Erdogan ya yi masa na cewa yana da hannu a kokarin juyin mulkin da ya faru a farkon watannan, da cewa abu ne da baida makama balle tushe.
Mallam Fethullah, ya rubuta cewa “A kida ta, itace addinin Islama addinine dake damawa da kowa, sabanin…..” malamin mai shekaru 75 ya rubuta, wanda kuma yake tsohon abokin shugaba Erdogan ne, da ya zabi zaman gudun hijira a jihar Pennsylvania dake gabashin Amurka tun shekara ta 1999. Bayan da dangantaka tsakanin su tayi tsami.
Turkiyya dai ta zargi Mallam Fethullah, da hada rikicin ‘yan tawayen da yayi sanadiyar rayukan mutane 290, kuma tana neman Amurka ta mayar da shi Turkiyya.
Sai dai kuma Amurka tace tana nazarin bukatar da Turkiyya ta aiko mata kan cewa Malamin yana da hannu a kokarin juyin mulkin, amma ba tayi alkawarin mayar da shi Turkiyya ba.