An tsara madatsar ruwa ta Kafin Zaki ne da nufin samar da ruwa ga manoman rani a sassan jihar Bauchi da Yobe da ma wasu bangarori na jihar Borno. Madatsar dai na daga cikin jerin Madatsun ruwa 12 dake karkashin kulawar hukumar kula da koramin Hadejia da Jama’are mai helkwata a birnin Kano.
Yanzu haka dai gwamnatin Tarayya tace tana jiran rahotan kwamitin kwararru game da wannan aiki na Kafin Zaki Dam, wanda zai bata damar sanin inda aka kwana a cewar ministan albarkatun ruwa Injiniya Sulaiman Husaini Adamu.
Samun nasarar wanzuwar madatsar ruwan Kafin Zaki Dam zai kara habaka ayyukan hukumar kula koramin Hadejia da Jama’are inji shugaban hukumar Sanata Mas’ud El Jibrin Doguwa, wanda yace idan anyi mutane dayawa zasu samu cin moriyar ta.
Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano.