Wata kungiyar rajin kare hakkin dan adam da ke Amurka ta ce tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa da kuma rashin bin diddigin aikata rashin gaskiya na cigaba da yin illa ga kasar Zimbabuwai.
Kungiayar ta “Human Rights Watch” mai hedikwata a birnin New York ta fadi yau Talata cewa ‘yan sanda sun yi watsi da kokekoken azabtarwa mai nasaba da siyasa.
Kungiyar ta ce gwamnati ba ta yi abin a zo a gani ba na dakile cin zarafin, kuma ta ce bin ba’asi game da rashin gaskiyar da su ka gabata da kuma wadanda ake yi yanzu wajibi ne matukar ana son a kawo karshen tashe-tashen hankula a Zimbabuwai a kuma kafa doka da oda.
Rahoton ya zargi jami’an tsaro da kuma jam’iyyar dadadden Shugaba Robert Mugabe da duka da cin zarafi da kuma kashe abokan adawa. Ta kuma soki gwamnatin rikon kwarya wadda jam’iyyar Firayim Minista Morgan Tsvangirai saboda gaza jaddada batun kare hakkin dan adam.
Kungiyar ta yi kira ga kasar Zimbabuwai cewa ta yi maza ta yi bincike ta kuma dau matakan ladabtarwa kan wadanda su ka aikata rashin daidai, komai matsayinsu ko mukaminsu.