Mutumin da duniya ta amince da shi a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a watan Nuwamba a kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara, ya kara tsawon wa’adin haramta safarar Cocoa zuwa kasashen waje har zuwa karshen wannan watan. Mr. Ouattara yana kiki-kakar mulki da Laurent Gbagbo, wanda ya ki sauka daga kan kujerar shugabancin kasar. Mr. Ouattara ya haramta fitar da Cocoa zuwa kasashen waje a watan Janairu, bisa fatar toshe kafar da Mr. Gbagbo yake samun kudaden shiga. Wa’adin haramcin na farko zai kare a wannan makon. A halin da ake ciki, fadan da ake gwabzawa a tsakanin magoya bayan shugabannin biyu ya kara matsawa cikin wata unguwar da ake kira Yopougon a birnin Abidjan, inda akasarin mazaunanta masu goyon bayan Mr. Gbagbo ne. A da, akasarin tashe-tashen hankualn da suka biyo bayan zabe a birnin Abidjan su na wakana ne a unguwannin magoya bayan Ouattara. Kungiyar tarrayar Afrika da Majalisar Dinkin Duniya da akasarin kasashen duniya su na goyon bayan Mr. Ouattara a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasar. Mr. Gbagbo kuwa ya dage a kan cewa shi ne ya lashe wannan zabe. Wani babban mashawarcin Gbagbo yace ba su yarda da shawarar da Kungiyar Tarayyar Afrika ta yanke ta amincewa da Ouattara a zaman shugaba ba.
Mutumin da duniya ta amince da shi a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a watan Nuwamba a kasar IC, Alassane Ouattara, ya kara tsawon wa’adin haramta safarar Cocoa zuwa kasashen waje