Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Bi Diddigin Lamarin AbdulJabbar Har Zuwa Karshe - Ganduje


Gwamna Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)
Gwamna Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)

"Kuma muna gode maku domin kun taka rawar gani. Babu shakka wannan Muqabala wacce aka shirya, Malamai sun yi aikin nasu na malanta." 

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin bin diddigin al'amarin AbdulJabbar Sheikh Nasiru Kabara har zuwa karshensa.

Ya yi wannan alwashin ne lokacin da ya kai gaisuwar Sallah ga Halifan Darikar Qadiriyyah, Sheikh Qariballah Sheikh Nasiru Kabara, a Gidan Qadiriyyah da ke Kabara, a Kano, ranar Juma'a da tawagarsa inda ya kara da cewa “babu shakka wannan yaki ne namu duka gaba daya."

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

"Kuma muna gode maku domin kun taka rawar gani. Babu shakka wannan Muqabala wacce aka shirya, Malamai sun yi aikin nasu na malanta."

Babban Sakataren yada labaran gwamnan jihar Kano Abba Anwar ne ya bayyana ziyarar ta Ganduje cikin wata sanarwa da ya fitar.

"Kuma sun nuna cewar su masana ne. Kuma ba sani kawai ba, su na aiki da sanin. Domin shi ilimi amfaninsa a yi aiki da shi. Akwai masu ilimi amma ba sa aiki da ilimi. shi ya sa ma mu ka samu kan mu a irin wannan shakiyancin."

Tun da farko Gwamna ya fadawa Halifa Qariballah cewar "na ji bayaninka a kan al'amurran da su ka taso na kare Shugabanmu, Shugaban talikai, Annabinmu, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam. babu shakka wannan yaki namu ne gaba daya."

Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara
Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara

Mako daya kenan bayan da aka gurfanar da AbdulJabbar a gaban kotu kan zargin da ake masa na yin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W.)

Kotun ta ba da umarnin a tsare shi zuwa ranar 28 da za a ci gaba da sauraren shari’ar.

A nasa jawabin Qariballah godiya ya yi da cewa "ina yi wa Maigirma Gwamna maraba da zuwa wannan gida nasa kuma a wannan laburare mai dogon tarihi."

"Ina so na yi wa Maigirma Gwamna wata jinjina da godiya bisa yadda ya dauki tuta ta kare Mutunci da Alfarma ta Shugaba Sallallahu Alaihi Wasallam a wannan yanayi da wannan lokaci," in ji Sheikh Qariballah.

Ya sake cewa "Mu na jinjina maka kwarai kuma mu na kara ce maka Allah Ya saka da alheri."

XS
SM
MD
LG