Gwamnatin jihar Kano ta musanta wasu rahotanni da ake dangantawa da uwargidan gwamna Farfesa Hafsat Umar Ganduje inda ake cewa ta ce Murtala Sule Garo ne zai maye gurbin Ganduje.
Garo shi ne kwamishinan ma'aikatar da ke kula da kananan hukukomi da masarautu a jihar ta Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Wata sanawa da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar ta ce babu kamshim gaskiya a labarin.
“Uwargidan Gwamna ta yi farin ciki ne kawai da aikin Garo wanda ta kira shi da kwamanda kuma saboda goyon bayansa ga manufofi da shirye -shiryen Gwamna Ganduje da gwamnatinsa a jihar.” Garba ya ce.
A cewar sanarwar, an murguda abun da ke cikin bidiyon ta hanyar yin wani labari na kirkira daga ciki, kuma mutane sun yi ta yada labarai da yawa musamman ta hanyar mutanen da suke kudurin aniyar haifar da rudani da tashin hankali don haifar da rarrabuwa a cikin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki a jihar.
“Kamar yadda ta yabawa Murtala Sule Garo saboda rawar da ya taka, Maimartaba ta kasance mai nuna yabo ga duk wani kwamishina ko ma'aikacin gwamnati wanda ke yin abin al'ajabi a yayin gudanar da aikinsa." In ji Garba.
Malam Garba ya ce, gwamnatin Ganduje ta mai da hankali ne kan kammalawa da aiwatar da manyan manufofi da shirye -shirye tare da muhimman ayyukan samar da ababen more rayuwa tsakanin yanzu zuwa 2023.
“Don haka muna kira ga mambobin jam’iyya da su yi watsi da jita -jitar da ake yadawa tare da karkatar da kuzarinsu wajen tallafawa gwamnatin don ci gaba da yi musu hidima da kyau.”