Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Katsina Tayi Hobbasa Wurin Magance Matsalar Ruwa


Rijiyar burtsatse a Katsina
Rijiyar burtsatse a Katsina

Shekara guda bayan gwamnatin Najeriya ta ayyana dokar ta ba ci a bangarorin samar da ruwa da tsaftar muhalli, gwamnatin jihar Katsina ta bi sahu wajen ayyana makamanciyar wannan doka a wadannan banagrori.

Yawaitar cututuka masu nasaba da ruwa da ‘yan Najeriya ke amfani dasu da kuma karancin tsaftar muhalli a galibin karkara da birane na daga cikin matsalolin da suka zaburar da gwamnatin ta Najeriya wajen ayyana dokar ta ba ci a wadannan banagrori.

Yayin bikin ayyana dokar a bara, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya umarci gwamnatocin jihohi su bi sahu domin cimma nasara.

Shekara guda bayan umarnin shugaban kasa, gwamnatin jihar Katsina ta ayyana dokar ta bacin a bangaren ruwa da tsaftar muhalli, lamarin dake zaman wani kudirin kawar da hanyoyin daukar cutuka da yada su a tsakanin al’uma.

Dangane da yawan kudaden aiwatar da wannan tsari da kuma hukumomi ko kungiyoyin ketare da zasu dafawa shirin, manajan daraktan hukumar samar da ruwa a yankunanan karkarar jihar ta katsina Engr. Aminu Dayyabu Safana yace yanzu ne gwamnati zata tantance adadin kudin da zata bukaci domin aiwatar da wannan shirin.

Tuni dai kwararru kan dabaru da kimiyyar samar da albarkatun ruwa ke tsokaci game da wannan kudiri na gwamnatoci a Najeriya. Engr. Yahaya Bala Karaye tsohon manajan daraktan hukumar bada ruwa ta jihar Kano na cikin kwararru da ke aiki da hukumomin ketare irin USAID, DFID da kuma UNICEF a fannin samar da ruwa a Najeriya.

Kudiri mai lamba 6 na shirin SDGs dake karkashin kulawar majalisar dinkin duniya shine ke dauke da bayanai kan muradin samar da tsaftar muhalli a sassan duniya wadda ake sa ran cimmawa nan da shekara ta 2030.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG