Babban jami’in tattara sakamakon zaben Gwamnan jihar Bayelsa, Farfesa Faraday Orunmwese, ya bayyana David Lyon na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba 2019, da kuri’a 352,552, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Duoye Diri, ya zo na biyu inda ya samu kuri’a 143,172.
Jim kadan bayan bayyana wannan sakamakon zaben gwamnan jihar ta Bayelsa, mutane sun fantsama kan tituna domin yin murna nasara akan wanda su ka zaba.
Sai dai a wani taron manema labarai gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Henry Dickson, ya ce ba’a gudanar da zaben a wasu wurare ba, kuma za su dauki matakin da ya dace.
Wani jami’in jam’iyyar PDP a jihar Bayelsa ya bayyana matsayin jam’iyyar, inda ya ce basu yadda da sakamakon zaben da aka bayyana ba domin alkaluman da su ke da su na zabe ba su ne aka bayyana ba.
Saurari cikakken rahoton wakilinmu Lamido Abubakar daga Yenagoa:
Facebook Forum