Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta ta jihar Kogi ta bada sanarwar jinkirta bayyana sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a jihar har zuwa safiyar yau litinin.
Kawo yanzu dai hukumar zaben ta samu sakamakon zabe daga kananan hukumomi 19 daga cikin 21 da ake dasu a jihar.
A wata matsaya da aka cimma tsakanin hukumar da kuma wakilan jam’iyyun siyasa, babban jami’in hukumar INEC na wucin gadi a zaben na kogi, kuma mataimakin shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Ibrahim Umar, ya ce hukuma tana jiran sakamakon zabe daga wasu kananan hukumomi gudu biyu da ake fuskantar matsalar zirga zirgan ababen hawa, domin sai anbi ta kan ruwa zuwa jihar Neja kafin a samu shiga ko fitowa daga wadannan lunguna.
Kakakin hukumar zaben ta INEC a jihar Kogi, Alhaji Ahmed Bagudu Biyambo, ya fadawa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa da zarar sun samu sakamakon kananan hukumomi biyun da suke jira, idan ya kai su bayyana wanda ya lashe zaben, za su sanar.
Saurari cikakken rahoton wakilinmu Babangida Jibril:
Facebook Forum