Gwamnatin Najeriya ta ce tana cigaba da bullo da tsare tsare na kawo wa jama'a sauki, musamman a wannan lokaci da ake ta yekuwar tsakanin rayuwa a sanadiyyar hauhawar farashin kayan bukatun jama'a. Wanan na cikin kasafin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana na Naira triliyan 2 da digo 3 na tallafi da kuma nufin farfado da tattalin arzikin kasar a sanadiyyar bullar cutar coronavirus.
Daga cikin kudin da aka wara domin wannan hidima, Naira biliyan 75 ne aka ke6e musamman domin talafa wa masu kanana da matsakaitan masana'antu, kamar yadda Shugaban Kula da Sha'anin Masana'antu, Dikko Umaru Radda ya yi karin haske yana cewa sai mutum yana da kamfani na kansa, wanda ya ke da ma'aikata uku zuwa sama, kuma kamfanin ya zama yana da rajista kafin ya amfana.
Idan ma mutum bashi da rajista, to Gwamnati za ta yi wa kamfanin rajista kyauta a Hukumar yi wa kamfanoni Rajista wato CAC, bugu da kari kuma shugaban wanan kamfani ya zama yana da asusun ajiya a banki tare da samun lambar BVN { Lambar Shaidar AJiya}.
Ita kuwa jagorar wanan shiri kuma Ministar Masana'antu, Maryam Yelwaji Katagum ta ce a wanan kokari da Gwamnati ta 6ullo da shi, za a tabbatar ba a bar kowa a baya ba, kuma za a debi masu kasuwancin sufuri, masu keke Napep, masu faci, masu sana'ar gyaran gashi, kitso da aski dubu 35 zuwa 40 a jihohin kasar baki daya. Kuma za a fara ne da zuba masu kudi Naira dubu 50 har na tsawon wattani uku.
To saidai daya daga cikin masu masana'antu mai zaman kansa a Kano, Habibu Lawal Kofar Wambai, ya ce kar Gwamnati ta yi tuya ta manta da albasa, inda ya bada shawarar a yi sanarwa a kakafen yada labarai da dandalin sada zumunta da kuma shafukan jaridu domin mutane su sani cewa kyauta ake yi wa 'yan Najeriya wannan tallafin, inda ya ce a baya an samu tirjiya a lokacin da Gwamnati ta fito da shirin you-win.
Wannan tallafi kyauta ne ga yan Najeriya ba bashi ba, kuma kashi 45 cikin dari na wadanda za su amfan mata ne masu kananan sana'o'i kuma kashi 5 a cikin su masu bukata ne na musamman.
Ga Madina Dauda da cikakken rahoton:
Facebook Forum