Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Fito Da Hanyar Biyan Kudin Haji Cikin Sauki


Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON)
Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON)

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta fito da wani shiri na adashin zuwa aikin hajji ga maniyyatan kasar, inda za su dinga adana kudi kadan-kadan har su biya kudin kujera.

Wannan ya biyo ne bayan kasancewar maniyyatan kasar ba su sami damar sauke farali ba a bana, sakamakon dokokin da kasar Saudi Arebiya ta saka na takaita aikin hajjin ga wadanda ke zaune a cikin kasar kadai, domin kaucewa cunkoson jama’a a dalilin annobar coronavirus.

Hakan kuma zai baiwa ‘yan kasar da dama da ba su da halin biyan kudin hajjin baki daya, damar su rika biya a hankali, taro-sisi, har a cimma biyan bukata.

Hajji
Hajji

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da biyan kudin hajjin ke neman gagarar mai karamin karfi sakamakon karuwar kudaden guzuri, wanda akasari tashin Farashin canji ke haddasawa.

Shugaban Hukumar Ahazan Zikirullahi Olakunle Hassan ya ce tun yanzu masu niyar zuwa aikin hajji a shekara mai zuwa za su iya fara ajiyar kudinsu a karkashin sabon tsarin, har zuwa lokacin da za su shirya gudanar da aikin hajjin ba tare da wata matsala ba.

Hukumar ta kaddamar da shirin ajiyar kudin ne tare da hadin gwiwar bankin Ja'iz wanda ya samar da ingantattun hanyoyin sadarwa ta yanar gizo don saukaka aiwatar da shirin.

Zikirullah ya ce yarjejeniyar wata sabuwar dabara ce da aka kirkira don saurin aiwatar da shirin, inda ya ce duk wanda ya yi wanan ajiya ba zai yi hasara ba domin ko baya ga amfani da kudin wajen yin ibada, haka ma zai amfana da ribar kasuwanci, kana kuma babu iyakancewa ga adadin abinda za'a ajiye ko shekarun da za'a yi ana ajiyar.

Jami'in Kula da adashin gatan Dr. Aliyu Tanko ya ce “mutum ya na iya yin rajistar dukkan iyalan sa sannan kuma ko Naira dubu daya ne ana iya ajiye wa.”

An kirkiro sabon tsarin ne a karkashin dokar da ta Kafa Hulumar Alhazai ta 2006 a matsayin shirin bayar da gudummuwa ga mabiya addinin Musulunci masu son zuwa aikin Hajji kuma basu da karfin biyan kudin a lokaci daya.

Shugabar Kungiyar Mata Musulmi ta kasa Hajiya Halima Jibril da ta wakilci mata a kaddamar da shirin, ta ce mata ma ba’a bar su a baya ba a sabon tsarin, akan haka ta yi kira ga al'umma da “su yi cikakken amfani da wannan dama da za su iya zuwa sauke farali a cikin sauki ba tare da wata damuwa ba.”

Hukumar Alhazan ta riga ta ba maniyata daman soma yin rajista a duk fadin kasar.

Babban bako a wajen bikin kaddarmar da shirin shi ne Sakataren Gwamnatin Taraiyya wanda Olusegun Adekunle ya wakilta.

Saurari cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Hukumomin Saudiyya Sun Shirya Karban Alhazai a Mina

Hukumomin Saudiyya Sun Shirya Karban Alhazai a Mina
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:05 0:00


Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG