Girzizar kasar mai karfin maki 7.5 wadda ta afkawa kudanci garin Porgera mai tazarar kilomita 90, ta karya gofofin wutar lantarki tare da lalata hanyoyi a fadin dan karamin tsibirin dake yankin Pacific Island, wadda ta katse hanyoyin sadarwa a mafi yawan sassan tsibirin dake tuddai inda nan ne grigizar tafi barna.
Jami’ai sun aika da tawagar ma’aikatan agajin gaggawa zuwa yankin Hela, ta jirage masu saukar ungulu domin su duba barnar da ta faru, su kuma tabbatar da mutanen da suka mutu.
Girgizar kasar ta tilastawa kamfanin Mai na ExxonMobil rufe ayyukansa a ma’aikatar kamfanin dake yankin, ind a yake ayyukan mai da iskar Gas.
Papua New Guinea na ‘daya daga cikin kasashen dake kan kunyar d a take haddasa girgizar kasa da ake kira "Ring of Fire" d a turanci a yankin na Tekun Pacific.
Facebook Forum