Fadar White House tace shirin da China take yi na janye wa’adin mulkin shugaban kasa, wani yunkurin da zai ba shugaba Xi Jinping ikon ci gaba da mulkin kasar har iya rayuwarshi, batu ne na cikin gida da ya shafi China ita kadai.
"Ina jin wannan shawara ce da China zata yanke bisa radin kanta, yadda taga yafi dacewa da kasarta" bisa ga cewar kakakin fadar White House Sarah Huckabee Sanders yayin ganawa da manema labarai jiya.
Wa’adin mulki abu ne da Trump yake goyon baya a nan Amurka, amma wannan batu ne da China zata yankewa kanta hukumci a kai, in ji ta.
Jam’iyyar kwaminis ta kasar China ta bada shawarar cire wa’adi biyu kan mulki na shugaban kasa daga kundin tsarin mulkin kasar, bisa ga rahotannin da kafofin sadarwa suka yayata ranar Lahadi.
Wannan zai karawa shugaba Xi karfi wanda tuni ake daukarsa a matsayin shugaban kasar China mafi tasiri a cikin shekaru da dama.
Jiya Litinin shugaban Amurka Donald Trump ya yabi Xi, tare da cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakaninsu, kuma yana matukar ganin kimar shugaban na China.
Facebook Forum