Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Mekziko Ya Fasa Zuwa Amurka Saboda Shirin Amurka Na Gina Katanga


Afghan Special forces patrol a deserted street during fighting with Taliban fighters, in Lashkar Gah, Helmand province, southern Afghanistan.
Afghan Special forces patrol a deserted street during fighting with Taliban fighters, in Lashkar Gah, Helmand province, southern Afghanistan.

A cigaba da takaddamar da ake yi tsakanin Shugaba Donald Trump na Amurka da Shugaban Mekziko Enrique Pena Nieto, saboda shirin Amurka na gina katanga tsakaninsu, Shugaban na Mekziko ya ce ya ma fasa zuwa Amurka.

Bayan musayar zafafan kalamai a makon da ya gabata, kan shirin gina katanka a kan iyakar Amurka da Mekziko (Mexico), Shugaban kasar Mekziko Enrique Pena Nieto ya soke shirin kai ziyara Fadar Shugaban Amurka ta White House, a cewar wani rahoton da jaridar Washington Post ta rubuta jiya Asabar.

Pena Nieto da Trump sun yi magana ranar Talata, inda su ka shafe lokaci mai yawa kan batun gina katangar a tsawon sa’a guda da su ka yi, a cewar majiyar da ta yi bayani ma jaridar ta Post.

Yayin da ya ke yakin neman zaben Shugaban kasa, Trump ya yi alkawarin cewa zai gina Katanga akan iyakar Amurka da Mexico don rage kwararowar bakin haure. Ya kuma gaya ma magoyansa da ke cike da sha’awar hakan cewa kasar Mexico za ta biya kudin gina katangar.

To saidai a tattaunawar da su ka yi ranar Talata, mutanen biyu sun yi muhawara kan wannan batu. Pena Nieto ya bukaci Shugaban na Amurka ya fito karara y ace kasar Mekziko ba za ta biya kudin gina katangar ba, to amma Trump ya ki.

Wani jami’in gwamnatin Mekziko ya ce Trump ya kuhula lokacin tattaunawa ta wayar, to amma wani jami’in gwamnatin Amurka ya karyata da cewa abin da ya faru kawai shi ne Trump ya yi takaicin hakan, a cewar jaridar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG