Hukumomin Faransa su na kokarin gaggawa na gano mutanen da suka aikata abinda shugaba Francois Hollande ya bayyana a zaman "ayyana yaki" a kan kasarsa, bisa fargabar cewa har yanzu mutanen da suka kulla wadannan munana hare-haren su na kitsa kai wasu nan gaba.
Kungiyar 'yan ta'adda ta ISIS ta dauki alhakin kai wadannan munanan hare-haren da aka kaddamar da su lokaci guda cikin daren Jumma'a a wurare shida a fadin birnin Paris, inda aka kashe mutane akalla 128, wasu da dama kuma su na kwance rai hannun Allah a asibiti.
Shi ma shugaba Hollande ya dora laifin hare-haren a kan kungiyar ISIS, wadda ta fito da kakkausar harshe tana sukar kasashen dake kokarin hana ta kafa abinda ta kira daular Musulunci a cikin kasashen Iraqi da Syria.
Amma wani jami'in yaki da ta'addanci na Faransa, ya ce har yanzu hukumomi su na kokarin su gano ko maharan da suka mutu a lokacin wannan farmakin mazauna kasar ta Faransa ne, da inda suka samu wadannan muggan bindigogi, sannan kuma abu mafi muhimmanci, ko su na da sauran 'yan'uwa dake shirin kai wasu hare-haren nan gaba.
An dauki tsauraran matakan tsaro a ko ina cikin kasar ta Faransa, a yayin da ake bin diddigin wadannan hare-haren.