Wasu ‘yan ta’adda sun kai hare-hare da aka kitsa lokaci guda a wurare dabam-dabam cikin daren Jumma’a a Paris, suka kashe mutane masu yawa ta amfani da bindigogi da kuma bama-bamai.
Mutane akalla 100 suka mutu a wuri guda, a bayan da ‘yan bindiga suka kai farmaki kan wani gidan wasa na birnin Paris, suka yi garkuwa da mutane masu yawa kafin ‘yan sanda su kutsa cikin ginin su kawo karshen wannan garkuwa.
An kashe biyu daga cikin maharan. Akwai ‘yan kallo har kimanin dubu daya a dakin wasa na Bataclan inda ‘yan bindigar suka katse wasan da wata kungiyar mawaka ta Amurka take yi, ta hanyar bude wuta da bindigogi kirar Kalashnikov. Mutane da yawa sun samu tserewa a lokacin da ake harbe-harben.
Daya daga cikin hare-haren bama-bamai kuma an kai ne dab da wani filin wasa inda shugaba Francois Hollande da kuma wasu dubban mutane suke kallon wani wasan kwallon kafa a tsakanin Faransa da Jamus. An ji karar tashin wannan bam a cikin filin wasan.
‘Yan sanda sun fitar da shugaba Hollande daga filin, amma a lokacin da aka tsayar da wasa sai ‘yan kallo suka sheka zuwa tsakiyar filin cike da tsoro.
Har ila yau kuma an kai hare-hare a kan wasu gidajen cin abinci da na barasa a wasu unguwannin dake shake da jama’a a babban birnin na Faransa.
Shugaba Hollande ya kira taron gaggawa na majalisar zartaswarsa, a bayan da ya bayar da umurnin a rufe duk wata hanyar shiga ko fita daga kasar, ko ta kasa ko ta sama ko ta ruwa.