Ana yin garkuwa da daruruwan mutane a wani dakin wasa, inda kararrakin harbe-harbe da bindigogi kirar Kalashnikov suka katse was an da wata kungiyar mawaka ta Amurka take yi a birnin Paris, babban birnin Faransa.
Rahotanni na baya-bayan nan sun ce an kasha mutane masu yawa, ko kuma ana yin garkuwa da su, yayin da wasu suka samu tserewa daga dakin was an.
Shugaba Francois Hollande y ace ya ayyana dokar-ta-baci a yayin da aka rufe dukkan iyakoki na kasa, da sama da ruwa, babu shiga ko fita daga kasar, matakin da ba a taba ganin irinsa ba cikin wannan karni a fadin Turai.
A nan Washington, shugaba Barack Obama yace a shirye Amurka take ta taimaka ta kowace irin hanyar da zata iya.
Wani jami'in ‘yan sandan Faransa ya fadawa VOA cikin daren nan cewa mutane 67 suka mutu a lokacin, amma kuma adadin sai karuwa yake yi. Rahotannin baya-bayan nan sun ce mutanen da suka mutu sun haura 100.
Ya zuwa yanzu, babu wanda ya dauki alhakin kai hare-haren. Wani shaida a cikin dakin was an yace maharani sun yi ta bude wuta kan jama’a, har sai da harsasansu suka kare, kuma sau uku suna sake lodin bindigogin suna ci gaba da bude wuta. Yace yana kusa da wata kofar fita, kuma ya samu nasarar tserewa a lokacin da maharani suka tsaya yin lodin bindigoginsu.