Shugaban yankin Falasdinu Mahmoud Abbas yace cikin watan satumba idan Allah ya kaimu zasu gabatarwa babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon, takardar neman kafa kasar Falasdinu.
Jiya talata ce Mr. Abbas ya bayyana haka a lokacin wata ziyara da ya kai Bosnia-Herzegovina, inda ya nemi kasar ta goyi bayan kduurin yankin na zama kasa ‘yantacciya. Daga nan ya tashi zuwa Lebanon, inda zai nemi karin goyon baya daga shugabannin Lebanon ciki har da Shugaba Michel Slieman, kan yunkurin kafa kasar.
Kasar Bosnia-Heregovina da Lebanon sune kasashe biyu da basu da kaujera ta din din din, a kwamitin sulhu. Mr. Abbas yana neman goyon bayan wakilan majalisar dinkin duniya su amince da bukatar kafa kasar Falasdinu, da zai kunshi yammacin kogin Jordan, zirin Gaza, da kuma gabashin birnin kudus, yankuna da isra’ila ta kama a yakin da suka gwabza a 1967.
Haka ma ranar talata, wakilan kasashe masun shiga tsakani a shawarwarin sulhu tsakanin ISra’ila da yankin falasdinu sun bayyana “matukar damuwa”, kan shirin isra’ila na fadada gine gine a yankunan yahudawa ‘yan share wuri zauna a yammacin kogin Jordan da kuma gabashin na birnin kudus. Masu shiga tsakanin da suka hada da wakilan majalisar dinkin Duniya,da tarayyar turai, Rasha da kuma Amurka.
Ranar litinin, Isra’ila ta bada sanarwar zata gina sabbin gidaje 277 a yammacin kogin Jordan, kwanaki kacal bayan ta amince da gina sabbin gidaje dubu daya da dari shida a gabashin birnin kudus.
A wasu rahotanni daga yankin, sojojin Isra’ila sun kashe falasdinawa biyu a zirin Gaza, daya a wani farmaki da jiragen yaki, guda kuma lokacinda aka ga ya doshi kan iyakar Isra’ila.