‘Yan sandan Pakistan sun ce wasu ‘yan bindiga su akalla 8 sun sace wani ba Amurke daga gidansa da sanyin safiyar yau asabar a birnin Lahore na gabashin kasar.
Ofishin jakadancin Amurka ya bayyana cewa mutumin da aka sace shi ne Warren Weinstein mai shekaru sittin da wani abu, kuma darekta a kasar Pakistan na wani kamfanin Amurka da ake kira J.E. Austin Associates mai bayar da shawarwari kan ayyukan raya kasa.
‘Yan sanda suka ce sun fahimci cewa Weinstein ya gama aikinsa a kasar Pakistan yana shirin barin kasar nan da jibi litinin. Komawarsa ma ke nan zuwa birnin Lahore daga Islamabad, babban birnin kasar.
Bayanin da Weinstein ya rubuta a shafinsa na LinkedIn a kan Internet ya nuna cewa tun shekarar 2004 yake zaune a birnin Lahore, yana jagorancin ayyukan da ake gudanarwa na raya kasa ma kamfanin tare da hadin kan hukumar talafawa kasashen waje ta Amurka da kuma gwamnatin Pakistan. Kamfanin J.E. Austin Associates yace Weinstein yayi shekaru 25 yana aikin raya kasashe a duniya.
‘Yan sandan Pakistan suka ce wadanda suka saci mutumin sun shawo kan masu gadin gidan Weinstein suka bude musu wata ‘yar kofa a bayan da suka ce sun kawo musu sadakar abincin sahur ne. Irin wannan sadaka ta abinci, ta zamo al’ada a lokacin azumin wata mai tsarki na Ramadan.