Amurka da kawayenta a turai suna kira ga shugaban Syria da yayi Murabus. Shugaban Amurka Barack Obama yana zargin shugaba Assad da “cin zarafi da yayyanka” mutanen da yake yiwa shugabanci, lamarinda wani jami’in majalisar Dinkin Duniya ya kira laifin cin zarafin bil’adama.
Jiya Alhamis Mr. Obama ya fidda sanarwar da take cewa lokaci yayi da shugaba Bashar na Syria “yayi murabus”. Haka kuma ya bada umurnin aza takunkumi kan kadarorin Syria dake Amurka, kuma ya haramtawa Amurkawa aiki ko zuba jari a Syria, haka kuma shugaban na Amurka ya haramtawa kamfanonin Amurka shigo da kaya da aka sarrafa daga albarkatunr mai daga Syria.
Haka ita ma babbar jakadiyar tarayyar Turai Catherine Ashton, ta yi kira ga shugaban Syria da yayi murabus, tana mai cewa bashi da sauran halicci a idanun jama’arsa.Tace tarayyar turai tana shirin fadada takunkumi kan Syria.Ingila, da Faransa, da Jamus da Canada duk sun yi kira ga shugaba Assad ya zakuda.
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai fara shawarwarin kakabawa Syria takunkumin karya tattalain arziki. Sai dai yana da wuya a shawo kan Rasha da China kada su hau kujerar naki a akamitin sulhun.
Da yake magana, jakadan Syria a Mahjalisar Dinkin Duniya Bashar Ja’afari, ya zargi Washington da wasu wakilan a kwamitin sulhu da kaddamar da abinda ya kira “yaki kan kasarsa ta fuskar difilomasiyya da wasu kafofi”.