ICPC hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ta yi diran mikiya akan kadarorin miliyoyin nera na wasu manyan ma'aikatan gwamnatin Najeriya su uku.
Wata sanarwa daga ofishin shugaban hukumar ta nuna cewa ma'aikatan uku na ma'aikatar raya yankin Niger Delta su ne Poloma Kabiru Nuhu da Mr. Landon Longi Yususfda kuma Daniel.
An samu Nuhu da wani fili a Abuja da kudinsa ya kai nera miliyan hamsin da wani katafaren gida da kudinsa ya kai nera miliyan cas'in da kuma filaye daban daban har guda 16 cikin birnin Abuja.
Sauran biyu an samesu da laifin mallakar dukiyoyi da filaye a Abuja da Fatakwal da zunduma zunduman motoci irin na isa. Yanzu duk hukumar ta kwacesu.
Kakakin hukumar Folu Olatimi ya kara bayani. Yace abun da suka yi yana kan ka'ida da dokokin hukumar. Kame kamen suna da nasaba ne da matsayin sabon shugaban kasa wanda ya kuduri yakar cin hanci da rashawa.
Yace kwana kwanan nan sun kwace kaddarorin wasu manyan jami'an hukumar tsaro ta farin kaya su goma sha biyu, wato Civil Defence ke nan. Yace sun buga sunayensu cikin jaridu. Daya daga cikin jami'an nada gidaje 62 cikin Abuja. Hukumar tana nan tana sa ido kan ma'aikatan gwamnati wadanda suke rayuwar da ta fi karfin albashinsu..
Mainasara Kogo Ibrahim ya nuna cewa abun da hukumar ta yi na kan ka'ida. A shari'ance abun na matakin bincike ne. Idan ana binciken laifi duk wani abu da aka tabbatar yana da alaka da kadarorin da aka wawure dole a kwacesu.
Ga karin bayani.