Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ko IBB a takaice ya gamsu da matakin sabuwar gwamnatin Muhammad Buhari akan yaki da cin hanci da rashawa.
Janar Babangida ya kuma gamsu matuka musamman ganin irin mutanen da shugaba Buhari ya zakulo ya sanya cikin kwamitin yaki da cin hanci da rashawa.
Yace mutanen da ya sa mutane ne da aka sansu a kasar. Ba baki ba ne.Idan an bi abubuwan da suka yi da kuma suke fada watakila zasu yi aiki, inji IBB.
Yau tsohon shugaban ya cika shekaru 74 da haihuwa. Yayinda yake jawabi a wurin bikin tunawa da haihuwarsa tsohon shugaban yace ya gamsu da yadda sojojin kasar ke fatattakar 'yan kungiyar Boko Haram yanzu.
Yakamata yanzu 'yan Najeriya su goyawa sojojin baya domin su samu karfin kawar da kungiyar gaba daya.
A fannin siyasa ma tsohon shugaban ya amince da yadda alamura ke tafiya saboda walwalar da 'yan kasar suke dashi .
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.