Shugaban kungiyar ta ECOWAS ko kuma CEDEAO, Marcel Alain de Souza, ya gayawa manema labarai a jiya Juma’a cewa, an tanadi dakaru na musamman wadanda su ke cikin shirin ko-ta- kwana.
Ya kuma kara da cewa an zabi kasar Senegal a matsayin wacce za ta jagoranci kawar da gwamnatin ta Jammeh, domin ita ce kasa da ke kewaye da Gambia ta bangarori uku.
Koda yake a baya kasar ta Senegal ta ce daukar matakin soji shi zai kasance zabi na karshe a yunkurin da ake yi na kokarin shawo kan rikicin siyasar kasar na Gambia.
A ranar 18 ga watan Janairun shekarar 2017 wa'adin shugaba Jammeh zai kawo karshe.
Shugaba Jammeh wanda ya mulki Gambia na tsawon shekaru 22, a baya ya amince da shan kayi a zaben da aka yi a watan Disamba, amma daga baya sai ya fake da cewa an tafka magudi a zaben.