'Yan adawan sun dora laifin kasawar gwamnatin kasar ne akan shugaban kasa Issoufou Mahammadou wanda suka ce cika alkawuran da yayiwa talakawa lokacin neman zabe ya faskareshi.
Alhaji Dudu Muhammadou na sabuwar jam'iyyar FDR Canji ya bada misalan gazawar gwamnatin Issoufou Mahammadou. Na farko shi ne batun samar da kwamciyar hankali a cikin kasar. Yace suna zaune lafiya da amma sai aka wayi gari shugaban kasar ya kawo masu rashin zama lafiya.
Kafin Issoufou ya hau mulki yayi alkawarin ba kowane yaro ilimi kyauta na shekaru goma sha shida. Yayi alkawarin bada magunguna kyauta wanda bai cika ba. Haka ma lamuran kasuwa ya tabarbare a arkashin gwamnatin Issoufou.
Jam'iyyun na adawa sun bukaci Shugaba Issoufou Mahammadou da ya sauka daga kujerar shgabancin kasar ta Nijar saboda a cewarsu ya gaza.
Saidai jam'iyyar PNDS mai mulki tayi watsi da bukatar ta 'yan adawa. Alhaji Umaru na PNDS din yace batun na 'yan adawan irin na wadanda dabara ta kubuce masu ne.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.