Da karfe goma-sha-biyun daren jiya Litnin din ne wa’adin mulki na biyu na shugaban ya kamalla, amma kuma wani kakakinsa, Barnabe Kikaya yace ce dole sai shugaban ya sauka daga mulki da karfe 12 na dare, kamata yayi a barshi ya wayi gari yana mulki.
Tuni dai Kotun Tsarin Mulki ta Congo ta yanke hukuncin cewa shugaba Kabila zai iya ci gaba da mulki har sai an yi sabon zabe, to amma sha-biyun dare na yi wasu mazauna birnin suka fara bushe-bushe don bada sanarwar cewa lokacin saukar shugaban fa ya zo.
Haka kuma an bada rahottanin jin karar harbe-harbe a yankuna da dama na kasar.
A cikin Kinshasha, babban birnin kasar, an yi tarukkan gangami da dama duk kuwa da haramcin irin wadanan tarukkan da gwamnati tayi.
An dai warwatsa sojoji ko ina cikin garin yanzu, yayinda ‘yan-sanda suka rinka watsa barknon tsohuwa don tarwatsa gungun mutanen dake zanga-zanga.