Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaman Da Shugaba Joseph Kabile Ke Yi Akan Mulki Baya Kan Ka'ida


Shugaba Joseph Kabila, na Jamhuriyar Demokuradiyyar kwango
Shugaba Joseph Kabila, na Jamhuriyar Demokuradiyyar kwango

Shugaban ‘yan jam’iyyar adawa na kasar Jamhuriyar dimokradiyyar Congo Etienne Tshisekedi, ya fada yau Talata cewa jama’ar kasar su dauki zaman da shugaba Joseph Kabila ke yi kan karagar mulki a matsayin na saba ka’ida wanda bai dace ba.

A wani sakon bidiyo da aka fidda ta Youtube, Tshisekedi ya kuma yi kira ga al’ummar kasar bi dauki matakin lumana wajen gujewa abinda ya kira juyin mulkin da kotun tsarin mulkin kasar ta daurewa gindi.

Kotu ta yanke hukunci cewa, Kabila zai iya cigaba da mulki har sai anyi zabe. Jam’iyya mai mulki ta bada shawara a gudanar da zabe a watan Afirilun shekarar 2018.

Mazaunan wasu sassan Kinshasa, babban birnin Congo, sun busa wusur da tsakar dare don nuna cewa lokacin barin kujerar mulkin Kabila ya yi. An kuma ji harbe-harben bindigogi a wasu gundumomin.

Mai ba shugaban kasa shawara Barnabe Kikaya ya fadi cewa “Nuna bukatar shugaba Kabila ya sauka daga karagar mulki da tsakar dare baya cikin kundin tsarin mulkin kasa.

XS
SM
MD
LG