Ma’aikatar tsaron cikin gida ta Rasha ta fada yau Litinin cewa bayan fararen hula, ‘yan tawayen Siriya na da damar yin amfani da hanyoyin fitar da mutane don barin garin Ghouta dake gabashin kasar da aka yiwa kawanya.
Wata sanarwa daga ma’aikatar ta ce mayakan za su iya daukar makaman su da iyalan su, su tafi, amma ba ta fayyace inda za su je ba.
Cigaba da tashin hankalin da ake samu a yankin ya kawo cikas a yarjejeniyar tsagaita wuta a Siriya da Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a yi, da kuma tsagaita wutar da Rasha ta ayyana duk rana don kai taimakon agajin jinkai da zummar ba fararen hula damar barin gabashin Ghouta.
Jiya Litinin ayarin motocin kai taimakon jinkai na kasa-da-kasa bai iya kai kayan gabashin Ghouta ba, bayan da dakarun gwamnati suka cigaba da lugudan wuta ta sama da ta kasa.
Facebook Forum