Kuri'un neman ra'ayoyin masu jefa kuri'a da aka ji a bayan da suka kada kuri'unsu jiya Lahadi a fadin kasar Italiya, sun nuna cewa babu wata jam'iyya guda da zata samu rinjaye a cikin majalisar dokoki, amma kuma jam'iyyu masu ra'ayoyin dake da farin jini a wurin jama'a sun samu karin kujeru masu yawa. Wannan zabe yana daya daga cikin wadanda suka fi rarraba kawunan al'ummar kasar a cikin 'yan shekarun nan.
Kamar yadda kuri'un neman ra'ayoyin suka nuna, jam'iyyar "Movimento 5 Stelle" mai akidar yin sauyi ga tsarin yadda al'amura ke gudana a kasar, ta taka rawar gani, musamman a yankin kudancin kasar inda jama'a suka fito fiye da yadda aka yi tsammani.
Jam'iyyar dai ana hasashen zata samu kashi 29 zuwa 31 na daukacin kuri'un da aka kada, abinda ke nufin cewa zata zamo babbar jam'iyya a cikin majalisar dokoki, sai dai kuma wannan ba zai ba ta sukunin samun rinjayen da har zata iya yin mulki ita kadanta ba.
Ita ko jam'iyyar "Democrat" mai ra'ayin sassauci, ta kokarta ta samun fiye da kashi 20 cikin 100, inda kuri'un neman ra'ayoyin ke nuna cewa watakila ta samu kimanin kashi 23 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Amma kuma gamayyar jam'iyyu masu ra'ayin 'yan mazan jiya ta Silvio Berlusconi, ta sha mata gaba, kuma ana kyautata zaton cewa zata kasance bangare mafi girma a cikin majalisar wakilan tarayya. Rawar da jam'iyyu masu ra'ayin 'yan mazan jiya suka taka a zaben na jiya lahadi, tamkar wata farfadowa ce mai ban mamaki ta Berlusconi mai shekaru 81 da haihuwa, wanda aka haramtawa rike wani mukamin siyasa har sai zuwa shekara mai zuwa, amma kuma wanda ake jin cewa zai taka muhimmiyar rawa a siyasar kasar.
Facebook Forum