Majalisar dinkin duniya, da kungiyar bada agajin gaggawa ta kasa da kasa Red Cross, sun bayyana cewa, jerin gwanon motocin da suka aika dauke da kayan agaji ya samu nasarar shiga yankin gabashin Ghouta dake Syria, yankin da yake hanun 'yan tawaye.
Kungiyar bada agajin gaggawa ta kasa da kasa yankin Syria ta ce manyan motocin guda 46 suna dauke da abinci wanda zai ciyar da mutane 27,500 da kayan magunguna amman kuma ofishin agaji na majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa an hana motocin daukar magunguna da dama wanda ka iya taimakawa rayuwar mutane.
Kungiyoyin agaji da dama sun koka a baya, kan yadda ake rage irin kayayyakin agaji suke dauka yayinda suke ayyukansu a Syria.Jerin gwanon na yau litinin shine na farko da aka bari ya shiga gabashin Ghouta a kusan makonni uku da suka wuce.
Mai Magana da yawun kungiyar bada agajin gaggawa Pawel Krzysiek, yace a lokacin da motocin suka samu nasarar shiga garin sai ya zam tamkar suna tsere ko rige-rige da lokaci.
Facebook Forum