Wasu daga cikin hotunan samun 'yancin kai da kuma gwamnatin farko ta shugaba Kwame Nkrumah a kasar Ghana
Jiya Ba Yau Ba: Ghana Ta Cika Shekaru 61 Da Samun 'Yancin Kai

1
Magajiyar Kent (Duchess of Kent) tana taka rawa tare da Kwame Nkrumah, firayim ministan Ghana na farko a wajen wata gagarumar liyafar da aka shirya a ranar 6 Maris 1957, domin murnar 'yancin kan kasar Ghana wanda ta samu a wannan rana.(AP Photo/Staff/Burroughs)

2
Kwame Nkrumah

3
Yarima Philip, magajin Edinburg, yana zaune tare da firayim ministan Ghana, Dr. Kwame Nkrumah a lokacin wata liyafar da aka shirya musamman domin zuwan Yariman birnin Accra a ranar 23 Nuwamba, 1959, domin ziyarar mako guda a Ghana. (AP Photo)

4
Firayim ministan Ghana, Dr. Kwame Nkrumah, da gwamna-janar na Ghana, Lord Listowel, suna tarbar Yarima Philip, Magajin Edinburg a lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Accra domin fara ziyarar mako guda a kasar Ghana, 23 Nuwamba, 1959. (AP Photo)